JAMIYYAR APM TA KADDAMAR DA KWAMITIN RIKON KWARYA A JIHAR BAUCHI

Daga Muazu Hardawa Bauchi
Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta ƙaddamar da kwamitin riƙon ƙwarya a Jihar Bauchi, tare da umartar mambobinsa da su sasanta rikice-rikicen cikin gida da kuma shirya zaɓen shugabannin jam’iyyar na dindindin a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
An gudanar da bikin ƙaddamar da kwamitin ne a ranar Talata a gidan gwamnatin jihar Bauchi, inda Mataimakin Gwamna, Hon. Mohammed Auwal Jatau, ya wakilci Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir a wajen taron da ya samu halartar wasu jiga-jigan jam’iyyar.
Cikin jawabinsa a wajen taron, Gwamna Bala Mohammed ya bayyana kafa kwamitin a matsayin wani muhimmin mataki na bunƙasa jam’iyyar da kuma ci gaban siyasar jihar baki ɗaya.
Ya buƙaci mambobin kwamitin da su ba da fifiko ga haɗin kai, nuna gaskiya don sauke nauyin da aka ɗora musu, maimakon amfani da muƙaman su wajen biyan buƙatun kan su.
Gwamnan ya bayyana naɗin nasu a matsayin wata dama ta sulhunta mambobin jam’iyyar da haɗa kansu, tare da jaddada muhimmancin gina ingantaccen tsarin siyasa da zai wakilci muradun al’umma.
A nasa jawabin, sabon shugaban kwamitin riƙon ƙwaryar APM a jihar, Shehu Adaji, ya gode wa shugabannin jam’iyyar na ƙasa bisa amincewar da suka nuna musu, tare da alƙawarin gudanar da ayyukan su cikin gaskiya, nuna aminci da jajircewa.
Ya kuma yaba wa shugabannin jam’iyyar na ƙasa, ƙananan hukumomi da unguwanni bisa gudummawar da suke bayarwa wajen ƙarfafa jam’iyyar tun daga tushe.
