ALHAJI ADO MAIKUZA YA BA, UWARGIDA HADIZA M.A. ABUBAKAR NAIRA MILYAN BIYU DON RABAWA MATA 200 A BAUCHI

Spread the love
ALHAJI ADO MAIKUZA YA BA, UWARGIDA HADIZA M.A. ABUBAKAR NAIRA MILYAN BIYU DON RABAWA MATA 200 A BAUCHI Daga Muazu Hardawa da Maryam Mohammed Sulaiman Bauchi Domin inganta gwagwarmayar yakin neman zaben tsohon gwamnan jihar Bauchi Bar. Mohammed Abdullahi Abubakar a karkashin tutar jamiyyar APC, Alhaji Ado Maikuza na hannun daman Bar. M.A. Abubakar ya bayar da tallafin naira Milyan biyu don rabawa Mata 200 da ke zaune a unguwar Fadamar mada Bauchi yadda kowace mata ta karbi naira dubu goma don inganta sana’a, saboda bunkasa tattalin arzikin su.
Uwargidan gwamnan Hajiya Hadiza M.A. Abubakar ta jagoranci raba kudin wa mata 200 Ranar Asabat 10/10/2026, yadda matan suka hadu don nuna goyon bayan su ga tafiyar makobcin nasu wato tsohon gwamna M.A.
Cikin jawabinsa Alhaji Ado Maikuza ya bayyana cewa ya samar da wannan Kudi ne daga aljihun sa don taimakawa wajen sauke hakkin makobtaka da kuma nuna goyon bayan mutanen yankin da ya fito na karamar hukumar Toro.
Ado Maikuza ya kara da cewa jam’iyyar APC tana da karfi a Toro kusan ita ke bin bayan karamar hukumar Bauchi a magoya baya. Don haka sun dauki mikatin ganin sun bayar da goyon bayan da ake bukata saboda Bar. Mohammed Abdullahi Abubakar ya dawo karo na biyu don kammala jagorancin jihar Bauchi.
Shima Alhaji Abdulmumini Bala Fanti cikin jawabinsa ya ja hankalin jama’a su ba da goyon baya don ganin Mohammed Abdullahi Abubakar ya dawo Mulki don kammala ayyukan da ya faro na ciyar da jihar Bauchi gaba.
Ya kara da cewa gwamnatin sa kowa ya sani babu magudi a cikin ta kuma ya bar gadon mulkin jihar Bauchi da bilyoyin kudi a cikin baitulmali, yadda gwamnati mai ci da wannan kudin ta fara gudanar da ayyukan ta da ake gani.
Itama Uwargidan tsohon gwamnan Hajiya Hadiza M.A. ta godewa matan Fadamar mada da dukkan yankunan jihar Bauchi. Don haka ta ce mai gidan ta ya shirya idan ya dawo karagar Mulki zai ba mutane mamaki ta hanyar gudanar da sabon samfirin salon mulkin ciyar da jama’a gaba.
Don haka ta bukaci kowa ya adana guri’arsa don fitowa yin zaben 2027 tare da bayar da goyon bayan su ga dawowar tsohon gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar karagar Mulkin jihar Bauchi don kammala ayyukan da ya faro a shekarun sa hudu na farkon mulkin jihar Bauchi a karkashin tutar jamiyyar APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *