Babbar mai Shari’a ta Saki Fursunoni 26 da Suka Shafe Shekaru 11 Ba Tare da Shari’a ba a Jihar Bauchi 

From Muazu Hardawa Bauchi
Kwamitin Harkokin Shari’a na Jihar Bauchi ya saki fursunoni 26 da ke jiran shari’a, ciki har da waɗanda suka shafe shekaru huɗu zuwa 11 a gidan gyaran tarbiyya ba tare da sun san matsayin su ba, saboda an gaza kammala shari’o’in su, wasu kuma babu wani bayani da ya shafi dalilin tsare su.
Alƙalin Alƙalan jihar Bauchi, Mai Shari’a Hajiya Rabi Talatu Umar, ce ta bayyana hakan yayin aikin duba gidajen gyaran tarbiyya domin bitar shari’o’in fursunonin a Gidan Yari sama da goma da ke Jihar Bauchi.
Mai Sharia Rabi Talatu Umar ta bayyana cewa a gidan yarin Bauchi binciken ya gano cewa ba a samun bayanan shari’ar wasu daga cikin tsararrun daga wurin ‘yan sanda masu gabatar da ƙara ko jinkirin hukunci a kotuna, yayin da wasu kuma sau ɗaya kawai aka gurfanar da su a kotu tun bayan tsare su tsawon lokaci.
Hajiya Rabi Talatu Umar ta bayyana cewa bai dace a ci gaba da tsare mutum na tsawon lokaci ba tare da an bi matakan shari’a da suka dace ba, don haka ta gargaɗi alkalan su kasance masu nuna gaskiya da adalci game da ayyukan su na alkalanci, saboda sauke nauyin da aka dora musu.
Babbar alkaliyar kotun Majistare Hajiya Safiya Musa, cikin jawabinta a madadin Hajiya Rabi Talatu Umar ta gargadi waɗanda aka saki da su guji aikata laifuka, domin kada su sake komawa gidan yari.
Don haka Safiya Musa ta musu nasiha da su kasance masu neman abin kan su ta hanyar ayyukan karfi da dako a kasuwanni ko neman taimakon jari a masallatai da su ke sallah don su dogara da kan su.
Tawagar babbar alkaliya Rabi Talatu Umar tana kai irin wannan ziyarar a gidajen gyaran tarbiyya sau hudu a shekara a gidajen yarin Jihar Bauchi da ke Bauchi da Ningi da jama’are da Nabordo da Darazo da Bogoro da Zaki da Azare da Misau da Alkaleri da sauran wuraren tsare kangararrun Yara.
Tana duba yadda Alkalai ke gudanar da Shari’a da yanayin da ake tsare da mutane.
A ziyarar Ranar laraba da alhamis an samu raguwar jinkirin shari’u saboda gidan yarin Azare kadai aka ziyarta madadin ziyartar akasarin gidajen.
Haka uma an iske alkalan sun yi hukunci ga tsararru 171 sai kuma wasu mutane kusan 20 da Shari’ar su ke tafiya ba tare da tsaiko ba.
A gidan gyaran tarbiyya na Bauchi ta sake tsararrun 26 ta kuma bukaci alkalai su gaggauta duba dukkan shari’u a yi hukuncin da ya dace a daina tsare mutane na tsawon lokaci.
Haka zalika Mai Shari’a Rabi Talatu Umar ta gargadi Yan sanda su rika gaggauta yin bincike don a samu gudanar da Shari’ar da suka kai gaban kotu, saboda wani lokacin suna kawo cikas wajen tafiyar hawainiya wa harkokin Shari’a lamarin da ke haifar da cikas wa Shari’ar da alkalan ke gudanarwa.
Tsararrun 26 da suka shaki iskar ‘yanci a gidan yarin Bauchi sun gode wa babbar mai Shari’a Rabi Talatu Umar saboda daukar matakin duba halin da suka shiga tsawon lokaci ta sake su.
Don haka jagoran su ya bayyana cewa sun dauki lamarin a matsayin kaddara da jarrabawa daga Allah kuma za su kasance mutane na gari idan sun koma garuruwan su.
Haka kuma sun yi mata adduah da fatar Allah ya kara mata daukaka a fannin aiki zuwa babban mataki a tarayya ko duniya a fannin Shari’a.
Kasancewar akwai babbar alkaliya Mai bin diddigin yadda ake tuhumar mutane a ma’aikatar Sharia ta jihar Bauchi Hajiya Sha’awanatu Yusuf wacce Allah ya mata rasuwa a kwanakin baya, saboda kowane lokaci da ita ake fita wannan aikin, kuma tana musu nasiha a kowane lokaci, itama an yi mata adduah da fatar Allah ya jikanta da rahama ya gafarta Mata.
