GWAMNA BALA YA WARE NAIRA BILYAN 11 DON BIYAN TSOFFIN MA’AIKATA KUDIN GIRATUTI A JIHAR BAUCHI
Daga Muazu Hardawa Bauchi
Tsoffin ma’aikata na cigaba da karɓar kuɗaɗen su na gratuity da suke bin gwamnatin jihar Bauchi bayan sun bar aiki tsawon lokaci ba su karbi hakkokin su na kudin ritaya ba,. Yadda gwamna Bala Mohammed Abdulkadir ya ware naira bilyan 11, don biyan irin waɗannan basuka da ke kan gwamnatin tun daga lokacin mulkin Malam Isa Yuguda.
Biyan kuɗaɗen na zuwa ne a daidai lokacin da sabbin ma’aikatan da gwamnatin Senator Bala Abdulkadir Mohammed ta ɗauka ke fara aiki, yayin da wasu ke ci gaba da tsallake matakai da sharuɗan tantancewa kafin ba su takardun kama aikin..
Gwamnatin jihar Bauchi ta kashe kimanin naira biliyan biyu da miliyan ɗari uku da sittin da tara 1.3b wajen biyan aƙalla ‘yan fansho dubu ɗaya da ɗari biyu da tamanin da biyar 1285 Wanda suka bar aiki a shekarar 2012/2013..
An biya kimanin tsoffin ma’aikatan jiha guda ɗari uku da saba’in da bakwai 377 da takwarorin su na ƙananan hukumomi aƙalla dubu ɗaya da ɗari da hamsin da ɗaya 1151.
An kuma kammala tantance wasu ƙarin guda dubu da ɗari biyu da tamanin da biyar 1285 a matakin jiha da kuma ɗari tara da fasalin da biyu 992 na ƙananan hukumomi, yayin da ɗari biyu da arba’in da uku 243 ba su bayyana a gaban kwamitin tantancewa ba.
Sai dai tsarin da aka yi, an ajiye kimanin naira miliyan ɗari uku da hamsin da ɗaya 351m na waɗanda ba su bayyana ba kuma duk wanda ya bayyana ya kuma tsallake tantancewar za’a biya shi nan take.
Biyan kuɗaɗen an ci gaba da tsoffin ma’aikatan shekarar 2014 zai ɗauki kimanin kwanaki biyar baya da tsari na musamman na sauraron koke-koken masu jinya da sauran su kafin a biya su hakkokin su.
Haka zalika Wanda suka rasu za a tantance magada don bayar da kudin ga kotuna ko hukumomin da suke lura da rabon gadon mutanen da aka tantance magadan su don a raba musu kudaden a matsayin gado.
