GWAMNA BALA YA UMARCI JAMI’AN TSARO, SU YAKI ’YAN TA’ADDA DA MASU HAKAR MA’ADINAI BA BISA KA’IDA BA

Spread the love

GWAMNA BALA YA UMARCI JAMI’AN TSARO, SU YAKI ’YAN TA’ADDA DA MASU HAKAR MA’ADINAI BA BISA KA’IDA BA

Daga Muazu Hardawa Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya umarci jami’an tsaro da su ƙara tsananta aikin sintirin haɗin gwuiwa a yankunan da ake fiskantar barazanar tsaro a wasu yankunan jihar Bauchi.
Zama na musamman da shugabannin hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro ya gudana a ranar alhamis 15/10/2026 a gidan gwamnatin jihar Bauchi.
Ya kara da cewa gwamnatin sa ba za ta lamunci ayyukan ’yan bindiga, da masu garkuwa da mutane da masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Gwamna Bala Mohammed ya bada umarnin ne yayin da yake jagorantar taron Majalisar Tsaro ta Jihar Bauchi a ɗakin taro na Majalisar Zartarwa da ke Gidan Gwamnatin jihar.
Taron ya samu halartar dukkan shugabannin hukumomin tsaro daga jihar da Maimartaba Sarkin Bauchi, wanda shi ne shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta jihar.
Gwamnan ya ce duk da kasancewar jihar Bauchi tana cikin jihohin da ke da kwanciyar hankali idan aka kwatanta da wasu maƙwabtan jihohi, hakan ba zai sa a yi sakaci ba.
Ya buƙaci jami’an tsaron da su faɗaɗa aiyyukan da aka gudanar har aka kai ga samun nasarori a Karamar Hukumar Alkaleri da sauran yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro, musamman dazuzzuka da yankunan da ke kan iyakoki.
Dangane da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, Gwamna Bala ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi sassauci ga duk wanda aka samu da hannu a irin wannan aiki ba, yana mai cewa babu wanda zai tsira daga hukunci saboda matsayinsa, ko tasiri ko alaƙa ta iyalinsa.
Ya kuma gargaɗi sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da su ƙarfafa aiyyukan tattara bayanan sirri kan duk wanda aka samu yana taimaka wa masu aikata laifuka ko taimakawa wajen haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba zai fuskanci hukuncin doka, har da yiwuwar tsige shi daga muƙaminsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *