Skip to content
The Syndicate News

Search news

Type to search stories, topics and pages.

Latest
General News

KUNGIYAR LAUYOYI MATA TA DUNIYA FIDA, TA BUKACI MUTANE SU RIKA TONA ASIRIN MASU CIN ZARAFIN JINSI A JIHAR BAUCHI

By 3 min read
KUNGIYAR LAUYOYI MATA TA DUNIYA FIDA, TA BUKACI MUTANE SU RIKA TONA ASIRIN MASU CIN ZARAFIN JINSI A JIHAR BAUCHI
Spread the love

KUNGIYAR LAUYOYI MATA TA DUNIYA FIDA, TA BUKACI MUTANE SU RIKA TONA ASIRIN MASU CIN ZARAFIN JINSI A JIHAR BAUCHI

Daga Muazu Hardawa Bauchi

Kungiyar Mata lauyoyi ta duniya FIDA reshen jihar Bauchi ta fara gudanar da gangamin kwanaki 15 domin wayar da Kan jama’a game da illolin cin zarafin jinsi da yadda za a magance matsalar a jihar Bauchi da Kasa baki daya.
Mataimakiyar shugabar kungiyar FIDA reshen jihar Bauchi Barista Safiya Musa Salisu kuma babbar alkali a kotun Majistare ta Fadamar mada ita ne ta bayyana haka a lokacin gudanar da gangamin a harabar babbar kotun jihar Bauchi.
Bar. Safiya Musa ta kara da cewa kungiyar FIDA NGO ce tana cin gashin kanta ne. Kuma suna gudanar da ayyukan su ba don neman riba ba sai don taimakawa marasa karfi a fannin Shari’a, saboda haka su ne ke hada kudi don gudanar da ayyukan kungiyar.
Ta kara da cewa ana fara gudanar da gangamin na tsawon kwanaki 16 ko ina a duniya daga ranar 25 ga watan Nuwamba zuwa ranar 5 ga Disamba na kowace shekara.
Majistare Hajiya Safiya Musa Salisu ta kara da cewa abin da ke tsaya musu a rai shine yadda idan an ci zarafin Mata ta hanyar fyade ko tozarta dan Adam babba ko Yaro, amma mutane ke boye lamarin basa bayyanawa don a bi wa mutum hakkin sa.
Don haka ta ce a yanzu kungiyar FIDA ta kudiri aniyar ganin mutum komai girman sa ko matsayin sa idan ya ci zarafin Mata ko namiji dole su sa a gurfanar da shi a gaban kotu don ya fiskanci kotu don a hukunta shi daidai laifin sa.
Ta ce ganin banza ke sa mutane cin zarafin jinsi wato Gender Base Violence a turance don haka daukar matakin magance lamarin ya zamo dole.
Bar. Safiya Musa ta bayyana cin zarafin jinsi na faruwa kan Yara Maza da Mata ko tsakanin ma’aurata ko tsakanin kowane nau’in mutane.
Don haka ta bukaci alkalai da lauyoyi da Yan jarida a taimaka don a magance matsalar wacce rashin hakurin wasu gurbatattun mutane ke haifarwa a cikin al’umma. Kuma samar da gyara Shi zai tsarkake al’umma.
Gangamin na bana ya gudana a wannan juma’a yadda manyan alkalai a jihar Bauchi suka halarta. Cikin su akwai Mai Shari’a Hajiya Binta Umar Faruk da Bar Laraba Hamisu da Bar Halima Yusuf da Bar. Asabe Sarauta da Bar. Safiya Doma da kuma Bar Maimuna Aliyu shugabar kungiyar Lauyoyi Mata ta Afirka wato AWLA.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *